Skip to main content

Hirar Soyayya Masu Dadi

Hirar Soyayya Masu Dadi: Domin samun sirrukan ƙauna:

Hirar soyayya masu dadi

Soyayya ruwan zuma, idan kasha ka ba masoyi. Ruwan soyayya idan an sha shi yana kawo jin nishadi da kuma annashuwa ga zuciya masoyi. Daga cikin abubuwan da ke sa soyayya ta zama mai armashi da son kasancewa da juna akwai hirar soyayya masu dadi.

Hirar soyayya masu dadi tana ƙara kusanci tsakanin masoya, sannan tana gina fahimta, da kuma kara danƙon soyayya a cikin zuciyar masoya. A yau wannan rubutu nawa ni sarkin soyayya na shafin Aminiya zai baku labarin masoya guda biyu da suke soyayya cikin jindaɗi. Babban maƙasudin wannan post shine na koyar da yadda ake hirar soyayya masu dadi tareda nuna muhimmancin hakan domin gina dangantaka mai ɗorewa.

Labarin Masoya Biyu: Fatima da Sulaiman

Fatima da Sulaiman masoya ne da suka fara soyayya cikin tsantsan kaunar juna, domin kowane lokaci masoyan cike suke da kewar juna. Ni tunda nake a zahiri ban taɓa ganin soyayya mai ban sha'awa irin tasu Domin sune tushen rubutun hirar soyayya masu dadi.

Tun fa a ranar da suka haɗu suka fahimci junansu sosai saboda idan ka gansu a ranar farko da suka fara haɗuwa sai ka rantse wannan sun shekara kamar biyu suna soyayya, wannan ne dalilin da yasa soyayyarsu ta kasance tamkar neman ruwa a sahara, domin gaskiya ba kasafai ake samun irinta ba.

Ranar wata Lahadi, bayan Sulaiman ya idar sallar Asuba, sai ya janyo Smart phone nasa ya kira Fatima domin ya mata barka da safiya. Budurwar da koda yaushe take sob kasancewa da masoyinta ai kunsan ba daɗewa zata ɗaga waya, hakan ne ya faru kuwa domin ringing ɗaya Fatima ta ɗaga wayar, nan fa hirar soyayya masu dadi ta soma tsakaninsu, kamar haka:

Sulaiman: Assalamu alaikum, annurin zuciyata. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin daya halicceki sannan ina fata ya tashe ki lafiya?

Fatima: Wa’alaikum salam, haske mai wanke dukkan ɗaci a zuciyata. na tashi kalau. Kai fa?

Sulaiman: Alhamdulillah. Babyna yanzu haka kawai ina kewanki ne. Ke fa a kullum kina bani mamaki. Uhm, shin wai me kika yimin haka ne da kullu-yaumin ba zan iya gushewa cikin tunaninki ba?

Fatima: (Ta yi wani guntun murmushi) To aini ba wani abu nayi ba, Allah ne kawai yake sona da kai shine koda yaushe soyayyata cikin zuciyarka take ƙaruwa. Ni yanda nake ji a kanka yafi haka hubbyna.

Sulaiman: Kin san wani abu? a kowace wayewar rana ina ƙara godewa Allah daya haɗa ni dake a matsayin masoyiya. Fatima, kin zamto haske mai goge duk wani baƙin cikin  zuciyata.

Fatima: Kullum daɗaɗan kalamanka suna sa zuciyata cikin farinciki mara yankewa. Ka sani cewa kai ne farin cikin rayuwata, Ina alfahari da kai.

Sulaiman: Yau inaso mu tattauna wani lamari a kanmu. Shin menene mafarkinki gameda rayuwarmu ta nan gaba habeebty?

Fatima: Kullum mafarkina shine mu gina gida mai cike da soyayya, fahimtar juna, da kuma zaman lafiya mai ɗorewa. Ina fatan zamu kasance tamkar abokai, masoya, sannan kuma iyaye nagari ga 'ya'yanmu.

Sulaiman: Ina roko ubangiji ya tabbatar mana da wannan mafarki naki. Ni kuma babban burina a wannan rayuwa shine in zama mutum wanda zai dinga faranta miki a koda yaushe.

Haka dai Hirar Soyayya Masu Dadi ta cigaba cikin jindadi da nishadi har suka yiwa juna sallama. Wannan shine ake kira da Hirar Soyayya Masu Dadi domin kuwa koda yaushe suna cikin faranta junansu da kalamai abun so, irin wannan tattaunawa babu shakka itace ke kara dankon soyayya tsakanin masoya.

Muhimmancin Hirar Soyayya Masu Dadi Ga Masoya:

Kara Kusanci da juna: Wannan haka yake Hirar soyayya masu dadi tana kara kusanci da danƙon soyayya a tsakanin masoya.

Zaman Lafiya: Tattaunawar soyayya mai dadi na rage duk wani irin tashin hankali da kuma sabani dake shiga tsakanin masoya, sabida matsawar akwai fahimtar juna to akwai zaman lafiya, hirar soyayya masu dadi kuwa na kawo fahimtar juna.

Kulawa: Babu ko shakka hirar soyayya tana nuni da yadda kake son masoyinka kuma kake kaunar son kasancewa tareda shi a kowane lokaci.

Tattaunawa ko shawara: Ana iya amfani da hirar soyayya masu dadi wajen tattauna burukan rayuwa da kuma neman shawarar masoyi akan wasu mafarkai naka.

Misalan Abubuwa Domin Hirar Soyayya Masu Dadi

1. Tambayoyi Na Soyayya:

"Wane abu ne mafi dadi da kake tunawa game da ni idan bama tare?"

"Menene dalilin da yasa ka ke ganin ba zaka taba samun kamata ba?"


2. Kalaman Soyayya:

"Kin san cewa babu mai cike da kyawawan halaye irin naki?"

"Kowace rana idan ina tareda ke, ji nake kamar wata sabuwar rayuwa ce a tareda ni."


3. Tsokana cikin Nishadi:

"ke dai kin fiye son agwaluma, mene ya sa haka wai?"

"Wai ni ko dai akwai alƙawarin aure tsakaninki da chocolate ne?"

Hanyoyin Bi Domin Inganta Hirar Soyayya Masu Dadi:

Kasance Mai Kula: Ki saurari masoyinki da kyau a duk lokacin da yake magana, sannan ki bashi amsa cikin girmamawa da tunani.

Amfani Da Kalamai Masu Dadi: Ki tabbata kowace magana taki tana cike da nuna da soyayya da kuma kulawa.

Tsokana cikin Nishadi: Kiyi masa shagwaɓa da tsokana cikin kwarewa domin samun nishadi tareda masoyinki. Wannan ma amfani ne na hirar soyayya masu dadi da masoyi.

Tambayi Masoyinki: Ko yaushe tambaya a soyayya tana nuna kulawa da neman sirrukan masoyinki.

Addu’a da Girmamawa: Ki kasance mai yi masa addu'a da nuna cewa kin damu da jindadinsa da kuma ɓacin ransa domin hakan na kara dankon soyayya.

Ku Gane Cewa:

Hirar soyayya masu dadi itace ginshikin gina soyayya mai dorewa da zaman lafiya domin zata baku dama kusan dukkan halayen masoyanku, kusan dukkan abinda suke so dama wanda basa so. Idan kuka yi dubi da Fatima da Sulaiman sun zama misali na yadda hirar soyayya mai dadi ke kara ƙauna da nishadi. Koda yaushe ku kasance masu yin amfani da kalamai masu dadi, tsokana a cikin soyayyarku, sannan ku nuna kulawa. Mun gode.

Comments

Popular posts from this blog

Azabar Daren Farko

Azabar Daren Farko: Daren farko na aure ya kasance wani dare ne mai matukar muhimmanci ga amarya da ango, duk da cewa cike yake da fargaba, jin kunyar juna, dama kuma jindaɗi ga sababbin ma'aurata . Daren ranar farko na cike da farinciki da annashuwa na shiga sabon babin rayuwa. Sai dai kash! wasu amaren suna tsoron azabar daren farko , baku da laifi kunsan ance dama Allah ɗaya gari banbam domin kuwa wasu ma'auratan kan sha dadi a wannan lokaci wasu kuwa kan fuskanci ƙalubale da wahala a wannan lokaci.  Kafin dai in wuce ina yi muku lale maraba da shigowa wannan shafin ilimi nawa kuma zanyi bayani dalla-dalla dangane da azabar daren farko, dalilan dake kawo azabar daren farko, yadda amarya zata shawo kan matsalar, da kuma hanyoyin da ya kamata amarya da ango subi domin tabbatar da cewa daren farkonsu ya kasance mai cike da daɗi da kuma kwanciyar hankali. Menene dalilin da yasa Daren Farko yakan zama mai wahala ne? Abubuwa da dama sukan iya kawo azabar daren farko wasu daga cik...

Wasa Da Nonon Amarya A Daren Farko

Wasa da Nonon Amarya a Daren Farko: Ranar daren farko rana ce ta musamman ga rayuwar auren sabbin ma’aurata, domin tana matukar tasiri wajen gina soyayya da amincewa tsakanin amarya da ango tun daga tushe. Daga cikin abubuwan dake ƙara ƙayatar da daren wannan rana shine sanin sirrin wasa da nonon amarya a daren farko— wanda hakan ke kawo jindaɗi da nishadi ga ma’aurata idan aka yishi da hikima. A cikin wannan post nawa ni malamar mata ta wannan gida, zan tattauna sannan nayi bayani akan yadda ake wasa da nonon amarya a daren farko, muhimmancinsa, hanyoyin da za'a bi don jin daɗin mu'amala da juna, da abubuwan da ya kamata a kiyaye. Meyasa Wasa da Nonon Amarya A Daren Farko Yake Da Muhimmanci? Wasa da nonon mace yana da muhimmanci saboda: (*). Kawo Nishaɗi da Jindaɗi – Nonon mace yana da yawan jijiyoyi masu sanya mace jin daɗi yayin shafa su, musamman idan ka iya shafawa da tsotsewa cikin salo da iyawa. (*). Ƙarfafa Soyayya – Wasa da nonon amarya a daren farko yana taimakawa waj...

Kalaman Soyayya Masu Kwantar Da Hankali

Kalaman Soyayya Masu Kwantar da Hankali: Domin Faranta Ran Masoyi: Soyayya tana da matuƙar muhimmanci a rayuwar kowane ɗan Adam, domin tana kawo farin ciki, kwanciyar hankali da nutsuwa. Duk wanda yake soyayya yana bukatar kalaman soyayya masu kwantar da hankali domin ƙarfafa dangantaka. Idan kina son faranta ran masoyinki, tofa ina miki albishir cewa kin zo inda ya dace domin samun kalaman soyayya masu kwantar da hankali. Da yardar ubangiji wadannan kalamai zasu yi miki aiki yanda kike so. Domin bayar da gudummawa da taka muhimmiyar rawa wajen inganta soyayyarki da abun sonki. A wannan rubutu nawa ni sarkin soyayya na wannan gida, zan koyar dake yadda ake amfani da kalaman soyayya masu kwantar da hankali domin nuna tsantsan kauna da nuna kulawa ga masoyinki, kuma zan koyar dake hanyoyin furta su, da kuma yadda suke tasiri ga dangantakar masoya. Meyasa Kalaman Soyayya Masu Kwantar da Hankali Suke da Muhimmanci? A cikin ladubban soyayya akwai wasu dalilai da yawa dake sa furtawa masoyi...