Skip to main content

Shagwaba A Soyayya

Yadda Ake Shagwaɓa a Soyayya Domin Yan'mata:

Shagwaba a soyayya

Soyayya itace masu iya magana suke cewa ruwan zuma. Wato tafi daɗi idan kasha sannan kaba masoyi. Shagwaba a soyayya wani bigire ce da ke kawo nishadi da jindadi a zuciyar masoya, musamman idan kin iya gudanar da ita cikin salo na kulawa da fahimtar sahibinki. Yawanci gaskiya mata aka fi sani da shagwaba a soyayya domin dama ko ban faɗa ba, tofa shagwaba a soyayya tafi dacewa daku mata.

Wasu lokutan maza suna yin shagwaba a soyayya kuma shagwaban maza sai ta baki dariya domin wasu kwata-kwata basu iya ba, amma wasu mazan suna iya shagwaba a soyayya yadda ya kamata. To dama dai ance kowa da kiwon daya karbe shi. Ɗaya daga cikin hanyoyin da ake kara danƙon ƙauna tsakanin masoya shine shagwaɓa a soyayya.

Ita kuwa Shagwaɓa a soyayya ba wani abu bace illa wata dabara da ake yi ta salon magana ko motsin jiki domin neman kulawa ta gaggawa daga masoyiya, wato malam shagwaba a soyayya yan'mata suna yinta ne domin ka kula dasu cikin gaggawa watau dai ina bukatar hankalinka ne lokaci guda. 

Shagwaba a soyayya na ƙara jin dadin zamantakewa a tsakanin masoya. Wannan blog post nawa mai suna (shagwaba a soyayya) zai koya miki yadda ake shagwaba a soyayya da matakan da ya kamata kibi domin tabbatar da hakan. Ina miki albishir da cewa idan kika laƙanci shagwaba a soyayya to tabbas zaki dinga sanya masoyinki cikin kewarki kullum, kuma hakan ze saka soyayyarku ta zama mai dorewa.

Menene Shagwaɓa a Soyayya?

A kalma mai sauki, shagwaɓa a soyayya na nufin nuna wasu halaye kodai na kulawa ko kuma na neman kulawa daga masoyi, irin rauni mai ban sha’awa, ko tsokana mai dadi da nufin a bayar da kulawa ko neman kulawa daga masoyi. Wannan halaye da muke kira shagwaba a soyayya na iya kasancewa ta hanyar maganganu masu dadi, nishadi, ko wani yanayin motsi dake sa masoyi farinciki da jin annashuwa.

Amfanin Shagwaɓa a Soyayya

Kara Dankon Soyayya: 
Shagwaɓa a soyayya tana kara nishadi a dangantakar masoya, tana sa masoya su ji dadin hira da juna sosai.

Shawo Kai: 
Yin shagwaba a soyayya zai baki dama ki janyo hankalin saurayinki koda kuwa kun samu matsala ne, to shagwaɓa a soyayya na iya kawo sassauci da sauƙi wajen shiryawa.

Son Kasancewa Da Juna: 
Iya dabbaƙa shagwaba a soyayya nasa masoyi ya ji sha’awar kasancewa tareda ke koyaushe.

Fahimtar Juna: 
Shagwaɓa a soyayya na taimakawa budurwa sosai wajen fahimtar masoyinta cikin wasa da dariya ba tare da wata matsala ba.

Hanyoyin Yin Shagwaɓa A Soyayya Domin Masoya:

1. Yin Amfani Da Kalamai Masu Dadi:
Ki adana duk wata kalma mai dadi dake a kwakwalwarki ki rufe ruf, har sai lokacin da kika haɗu da sahibin ranki sai ki amayar masa dasu cikin lumana.

Lokacin yin shagwaba a soyayya ki yawaita amfani da kalmomi kamar "Masoyina," "Mukullin Zuciyata," ko "Mai sona." domin Kalmomin soyayya nada tasiri matuka wajen janyo hankalin saurayi da nishadantar dashi.

Ki yiwa Masoyinki shagwaɓa a soyayya ta hanyar tsokanarsa da wasa cikin nishadi, kamar:

"Wai shikenan yanzu zaka tafi, bafa ka goya Ni ba ?"
Irin wannan maganar shagwaba a soyayya tana motsa masoyi cikin sauƙi ya nuna kulawarsa gareki.

3. Bayar Da Kulawa:
Shagwaɓa a soyayya ta hanyar kula da masoyinki misali kamar shafa kansa, tambayar lafiyarsa da kuma lura da wani ƙaramin canji wanda zai iya faranta masa rai.

4. Yin Magana Cikin Taushi:
Ki kasance mai nuna masa so cikin murya mai taushi da nishadi kamar:

"Don Allah kar ka rabu dani, ka san fa kai ne farin cikina."
Irin wannan shagwaɓa tana sa masoyi jin dadin kasancewa tareda ke.

Cikin shagwaɓa ki dinga yiwa Masoyinki addu’a da fatan alheri kamar:

"Allah ya ja zamaninka shugabana, ni fa kullum ina cikin alfahari da kai."
Hakan yana nuni da yadda kike so da kaunar masoyinki.

6. Nuna Rauni:
Cikin shagwaba a soyayya Ki dinga nuna cewa kin dogara da masoyi a wasu lokutan ba koda yaushe ba. Misali:

"Ka san fa ba zan iya yin komai ba idan babu kai."

7. Yi Masa Kyauta Ko Ƙarama ce:
Yana daga cikin amfanin shagwaba a soyayya ki samu yardar sa, misali , Ki sayi abinda masoyinka yake so ko yi masa wani abu da yake matukar so. Karamin abinda zaki iya yiwa Masoyinki kyauta dashi shine "Turare" Wallahi maza na kaunar turare musamman idan budurwarsu tayi musu kyauta. Idan kin tashi yin kyautar kice masa:

"Na san zaka so wannan Habibina, amma ka ce min 'Na gode' Cike da shagwaɓa zaki faɗa."

Lokutan Da Suka Fi Daɗi Domin Yin Shagwaɓa a Soyayya:

(*) Yayinda kuke a cikin nishadi.

(*) Lokacin da kike son lallaɓa saurayinki ko mijinki akan wani abu da kike so ya Miki.

(*) Yayin da kike son janyo hankalin masoyinki.

(*) Sa'in da kike  bukatar kulawarsa to Kiyi masa shagwaba a soyayya.

Abubuwan Da Zaki Gujewa Lokacin Shagwaɓa

(*) Kada a shagwaɓarki ta zama kamar shirme ko shashanci ga masoyi.

(*) Kada ki yarda shagwaɓa a soyayya tayi yawa domin hakan zai zama kamar nuna gazawa ko rashin hankali. Saboda ba koda yaushe ake shagwaba ba.

(*) Kar ki kuskura ki yiwa masoyi shagwaɓa a soyayya idan baya cikin yanayi mai daɗi.

Ki Sani Cewa

Shagwaɓa a soyayya hanya ce mai kyau ta ƙara gina dankon soyayya da ƙara nishadi a rayuwar masoya. Musamman Idan aka yita cikin hikima, tana sa soyayya ta ƙara ƙarko da ƙarfi, kuma masoyi zai ji cewa yana da muhimmanci a rayuwa.

Comments

Popular posts from this blog

Azabar Daren Farko

Azabar Daren Farko: Daren farko na aure ya kasance wani dare ne mai matukar muhimmanci ga amarya da ango, duk da cewa cike yake da fargaba, jin kunyar juna, dama kuma jindaɗi ga sababbin ma'aurata . Daren ranar farko na cike da farinciki da annashuwa na shiga sabon babin rayuwa. Sai dai kash! wasu amaren suna tsoron azabar daren farko , baku da laifi kunsan ance dama Allah ɗaya gari banbam domin kuwa wasu ma'auratan kan sha dadi a wannan lokaci wasu kuwa kan fuskanci ƙalubale da wahala a wannan lokaci.  Kafin dai in wuce ina yi muku lale maraba da shigowa wannan shafin ilimi nawa kuma zanyi bayani dalla-dalla dangane da azabar daren farko, dalilan dake kawo azabar daren farko, yadda amarya zata shawo kan matsalar, da kuma hanyoyin da ya kamata amarya da ango subi domin tabbatar da cewa daren farkonsu ya kasance mai cike da daɗi da kuma kwanciyar hankali. Menene dalilin da yasa Daren Farko yakan zama mai wahala ne? Abubuwa da dama sukan iya kawo azabar daren farko wasu daga cik...

Wasa Da Nonon Amarya A Daren Farko

Wasa da Nonon Amarya a Daren Farko: Ranar daren farko rana ce ta musamman ga rayuwar auren sabbin ma’aurata, domin tana matukar tasiri wajen gina soyayya da amincewa tsakanin amarya da ango tun daga tushe. Daga cikin abubuwan dake ƙara ƙayatar da daren wannan rana shine sanin sirrin wasa da nonon amarya a daren farko— wanda hakan ke kawo jindaɗi da nishadi ga ma’aurata idan aka yishi da hikima. A cikin wannan post nawa ni malamar mata ta wannan gida, zan tattauna sannan nayi bayani akan yadda ake wasa da nonon amarya a daren farko, muhimmancinsa, hanyoyin da za'a bi don jin daɗin mu'amala da juna, da abubuwan da ya kamata a kiyaye. Meyasa Wasa da Nonon Amarya A Daren Farko Yake Da Muhimmanci? Wasa da nonon mace yana da muhimmanci saboda: (*). Kawo Nishaɗi da Jindaɗi – Nonon mace yana da yawan jijiyoyi masu sanya mace jin daɗi yayin shafa su, musamman idan ka iya shafawa da tsotsewa cikin salo da iyawa. (*). Ƙarfafa Soyayya – Wasa da nonon amarya a daren farko yana taimakawa waj...

Kuka A Daren Farko

Menene dalilin da yasa mata keyin kuka a daren farko? Daren farko na aure musamman ga amare wani lokaci ne mai cike da tunanin yan’uwa da kuma fargaba, wanda hakan na iya kawo kuka a daren farko. Sannan kuma akwai   jin daɗi, da kuma sauye-sauyen rayuwa, wanda yarinya bata zama gani ba. Ga wasu amaren, wannan rana ta farko takan iya haifar da kuka – wanda kan faru saboda dalilai daban-daban da suka shafi nutsuwar zuciya, yanayin sabo na amaraya, ko ma wasu abubuwa masu kama da haka. A cikin wannan rubutu mai taken kuka a daren a daren farko nawa ni malamar mata ta wannan gida mai aminci, zanyi bayani mai kyau akan dalilan da ke haifar da kuka a daren farko , da kuma yadda maza angwaye za su fahimci lamarin, da kuma hanyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da cewa daren farko ya kasance mai kyau ga duka ma’auratan, wato amarya da ango. Ga wasu dalilan da ke sa amare kuka a daren farko Bugun zuciya (sakamakon rashin sabo) Amare da yawa na iya yin kuka a daren farko, saboda ra...