Skip to main content

Wasa Da Nonon Amarya A Daren Farko

Wasa da Nonon Amarya a Daren Farko:


Ranar daren farko rana ce ta musamman ga rayuwar auren sabbin ma’aurata, domin tana matukar tasiri wajen gina soyayya da amincewa tsakanin amarya da ango tun daga tushe. Daga cikin abubuwan dake ƙara ƙayatar da daren wannan rana shine sanin sirrin wasa da nonon amarya a daren farko— wanda hakan ke kawo jindaɗi da nishadi ga ma’aurata idan aka yishi da hikima.

A cikin wannan post nawa ni malamar mata ta wannan gida, zan tattauna sannan nayi bayani akan yadda ake wasa da nonon amarya a daren farko, muhimmancinsa, hanyoyin da za'a bi don jin daɗin mu'amala da juna, da abubuwan da ya kamata a kiyaye.

Meyasa Wasa da Nonon Amarya A Daren Farko Yake Da Muhimmanci?

Wasa da nonon mace yana da muhimmanci saboda:

(*). Kawo Nishaɗi da Jindaɗi – Nonon mace yana da yawan jijiyoyi masu sanya mace jin daɗi yayin shafa su, musamman idan ka iya shafawa da tsotsewa cikin salo da iyawa.

(*). Ƙarfafa Soyayya – Wasa da nonon amarya a daren farko yana taimakawa wajen rage fargaba da kunya a tsakanin sabbin ma’aurata.

(*). Taimakawa Jikin Mace – Wasa da nonon amarya a daren farko yana ƙara yawan ruwan ni'ima a jikin mace, wanda ke hana mace jin zafi yayinda ango yake jima’i da ita.

(*). Ƙara Sha’awa – Idan aka yi wasa da nonon  amarya da kyau kafin jima'i, hakan yana ƙara mata sha’awa da kuzarin karbar gugar mijinta yadda ya kamata.

Yaya Ake Wasa da Nonon Amarya a Daren Farko?

Domin jin daɗin wasa da nonon amarya a daren farko, shine dalilin da yasa yana da kyau ango ya kasance mai lallashi da kula da yadda matarsa ke jin daɗin abinda yake mata. Ga wasu hanyoyi da za'a iya bi:

1. Shafa Nononta a Hankali

Ka fara shafa nononta da hannuwanka biyu cikin nutsuwa kuma a hankali.

Ka dinga amfani da yatsun hannunka kana ɗan murza kan nonon a hankali, ba tareda da matsawa da karfi ba.

Kayi wasa da kan nonon amarya a hankali domin yana saka mace jindaɗi har ma da sambatu.

2. Tsotsar Nononta a Sannu

Bayan ka gama wasa da nonon amarya a daren farko a hankali, sai kayi amfani da bakinka ka fara tsotsarsu cikin nutsuwa.

Kada kayi mata da sauri ko ka dinga tsotsa da karfi, domin hakan na iya kawo mata jin zafi.

Idan amaryarka tana jindaɗi, zata iya nuna hakan ta hanyar nishi ko fitar da wani sauti mai nuna alamun tana jindaɗin abinda kake yi mata.

3. Amfani da Baki da Harshe

Kana iya amfani da bakinka ko harshenka wajen shan nononta da leɓɓa ko harshe domin ƙara mata jindaɗi.

Ka dinga wasa da harshenka akan nonon nata domin hakan na ƙara sha’awa yayin wasa da nonon amarya a daren farko.

Idan amarya tana nuna tana jindaɗin abinda kake mata, zaka iya cigaba da wasa da nonon amarya a daren idan kaga haka da haɗawa da sassan jikinta domin ƙara ƙayatar da ita.

4. Kula da Yanayin Amarya

Kowane jikin mace yanada irin nasa yanayin, saboda haka yana da kyau ka lura da yadda amaryarka take reaction akan abinda kake yi mata wato wasa da nonon amarya a daren farko da kake yi.

Idan har amarya tana nuna rashin jindaɗi, ya kamata ka sauya salon wasan da kake yi ko  ka tambayeta don fahimtar abin da take so.

Abubuwan da Ya Kamata Ango Ka Kiyaye

Kada ka dinga yin wasa da nonon amarya a daren farko da karfi – Saboda nonon mace nada taushi, saboda hakan na iya sanya mata jin ciwo da raɗaɗi.

Kada kayi wasa da nonon amarya a daren farko ba tareda amincewarta ba – koda yaushe yana kyau ma’aurata su kasance masu fahimtar juna, idan amarya tana jin kunya, yana da kyau miji ya ƙara mata kwarin gwiwa sannan yabi ta a hankali.

A kiyaye tsafta – Kafin ka fara wasa da nonon amarya a daren, yanada kyau ango baki da hannuwanka su kasance masu tsafta da ƙamshi domin kaucewa cututtuka.

Kada ka dage idan bata jin daɗi – Idan amarya ba ta jindaɗi da abinda kake yi, yana da kyau a rabu da ita har sai ta nema ko ta fahimci abinda kake yi mata ta fuskar ilimin jima'i.

Wasa da nonon amarya a daren farko na iya ƙara soyayya da shakuwa a tsakanin ma’aurata, musamman idan aka yi cikin nutsuwa da lumana. Yana da kyau ango ya fahimci cewa ba dole bane amarya taji daɗin hakan, don haka yana da kyau kabi komai a hankali kuma da mutunta juna.

Comments

Popular posts from this blog

Azabar Daren Farko

Azabar Daren Farko: Daren farko na aure ya kasance wani dare ne mai matukar muhimmanci ga amarya da ango, duk da cewa cike yake da fargaba, jin kunyar juna, dama kuma jindaɗi ga sababbin ma'aurata . Daren ranar farko na cike da farinciki da annashuwa na shiga sabon babin rayuwa. Sai dai kash! wasu amaren suna tsoron azabar daren farko , baku da laifi kunsan ance dama Allah ɗaya gari banbam domin kuwa wasu ma'auratan kan sha dadi a wannan lokaci wasu kuwa kan fuskanci ƙalubale da wahala a wannan lokaci.  Kafin dai in wuce ina yi muku lale maraba da shigowa wannan shafin ilimi nawa kuma zanyi bayani dalla-dalla dangane da azabar daren farko, dalilan dake kawo azabar daren farko, yadda amarya zata shawo kan matsalar, da kuma hanyoyin da ya kamata amarya da ango subi domin tabbatar da cewa daren farkonsu ya kasance mai cike da daɗi da kuma kwanciyar hankali. Menene dalilin da yasa Daren Farko yakan zama mai wahala ne? Abubuwa da dama sukan iya kawo azabar daren farko wasu daga cik...

Kalaman Soyayya Masu Kwantar Da Hankali

Kalaman Soyayya Masu Kwantar da Hankali: Domin Faranta Ran Masoyi: Soyayya tana da matuƙar muhimmanci a rayuwar kowane ɗan Adam, domin tana kawo farin ciki, kwanciyar hankali da nutsuwa. Duk wanda yake soyayya yana bukatar kalaman soyayya masu kwantar da hankali domin ƙarfafa dangantaka. Idan kina son faranta ran masoyinki, tofa ina miki albishir cewa kin zo inda ya dace domin samun kalaman soyayya masu kwantar da hankali. Da yardar ubangiji wadannan kalamai zasu yi miki aiki yanda kike so. Domin bayar da gudummawa da taka muhimmiyar rawa wajen inganta soyayyarki da abun sonki. A wannan rubutu nawa ni sarkin soyayya na wannan gida, zan koyar dake yadda ake amfani da kalaman soyayya masu kwantar da hankali domin nuna tsantsan kauna da nuna kulawa ga masoyinki, kuma zan koyar dake hanyoyin furta su, da kuma yadda suke tasiri ga dangantakar masoya. Meyasa Kalaman Soyayya Masu Kwantar da Hankali Suke da Muhimmanci? A cikin ladubban soyayya akwai wasu dalilai da yawa dake sa furtawa masoyi...