Skip to main content

Zubar Da Ciki Da Gishiri

Zubar da ciki da gishiri: Illolin Amfani da Hanyoyin Gida Wajen Sauke Ciki:

Zubar da ciki da gishiri

A gaskiya ayi sani cewa zubar da ciki ba batun da ya kamata a dauka da wasa bane, kuma amfani da hanyoyin gida kamar gishiri ko wasu sinadarai na gida na iya jawo matsaloli masu tsanani ga lafiyar mace. Wannan blog post ɗin nawa na yau zai yi bayani kan illolin amfani da hanyoyin gida wajen zubar da ciki da gishiri, muhimmancin neman taimakon likita, da kuma wasu dabaru da zaki iya amfani dasu domin shirya kanki cikin aminci.

Shin Zai Yiwu a Zubar da Ciki da Gishiri?

A fannin likitanci, babu wata hujja ko bincike daya tabbatar da cewa zubar da ciki da gishiri na aiki. Duk da cewa wasu mutane suna gwada wannan hanya, to ayi sani cewa hakan yana da matukar haɗari sosai ga lafiyar mace. Amfani da zubar da ciki da gishiri ko wasu kayan gida don zubar da ciki ba hanya ce mai lafiya ko inganci ba, kuma yana iya kawowa mace matsaloli kamar haka:

(*). Zubar da Jini Mai Yawa: Amfani da hanyar zubar da ciki da gishiri na iya haddasa matsalar zubar da jini daga gaban mace wanda ka iya haddasa barazana ga rayuwa.

(*). Cutar Mahaifa: Zubar da ciki da gishiri ko wata hanya ta gargajiya ba bisa ka'ida ba na iya haifar da ciwon mahaifa, wanda zai iya jawo rashin haihuwa a nan gaba.

(*). Infection (Cutar Sanyi): Amfani da hanyoyi domin zubar da ciki wanda basa da wani tushe mai kyau na iya haifar miki da cutar sanyi ko amfani da hanyoyin gida yana iya sa mace ta kamu da cututtuka masu tsanani kamar tetanus ko sepsis.

(*). Mutuwa: A wasu lokutan ma kokarin zubar da ciki da gishiri ba tareda taimakon likita ba cikin gaggawa yana iya kaiwa ga mutuwar mace.

Muhimmancin Neman Taimakon Likita:

Idan mace tana cikin wani hali da take buƙatar kula da juna biyu ko hanyar da zata iya zubar da ciki, to ya kamata ta nemi taimakon likita ko wani ƙwararren ma’aikacin lafiya. Likitoci zasu iya bayar da shawara kan mafi kyawun hanya data shafi zubar da ciki, ko wata matsalar lafiya, ba tareda jefa mace cikin haɗari ba.

A cikin ƙasarmu Najeriya, dokokin zubar da ciki suna da tsauri sosai, sai dai idan ya zama tilas ko idan rayuwar mace tana cikin haɗari. Amma idan akwai wata damuwa dake damun mai ciki, neman shawara daga ƙwararren likita  shine hanyar tabbatar da lafiya ga kowace mace mai ciki.

Hanyoyin Da Za'a Iya Bi Domin Kariya:

Idan kin tabbatar da cewa baki shirya samun ciki ba, akwai hanyoyin da zaki iya amfani da su domin kiyaye ɗaukar ciki cikin koshin lafiya da lumana:

(*). Amfani da Kayan (Contraceptives): Ba bukatar zubar da ciki da gishiri domin wadannan sun haɗa da kwayoyi, allurai, ko na'urar IUD da ake sakawa a mahaifa kinga kenan ba zaki ɗauki ciki ba tun da farko.

(*). Shawara da Iyali: Kuyi shawara kai da iyalinka akan tazarar haihuwa ko a nemi shawara daga ƙwararrun ma'aikatan lafiya kan yadda za'a bi wani tsari na iyali domin tazarar haihuwa.

(*). Sanin Lokacin Haihuwa: Mata da yawa sun san duk wasu alamu na idan suna dauke da juna biyu tun kafin ya kai wani munzali, domin hakan zai baki dama kiyi abinda ya kamata tun kafin lokaci ya kure.

(*). Bin Tsari Mai Kyau: Zaɓar tsari mai Kyau shine yafi dacewa don kauce wa haɗari ko wani sakamakon da ba a shirya masa ba.

Illar Amfani Da Zubar da ciki da gishiri ko kayan Gida:

Batun amfani zubar da ciki da gishiri ko wasu sinadarai na gida wajen zubar da ciki abu ne wanda yake faruwa ba tareda ilimi ba, domin haka a kiyaye lafiya.

(*). Ilmantarwa da Fadakarwa: Ya zama wajibi ga gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu su gudanar da wayar da kan jama’a kan muhimmancin neman taimakon likita da kuma hanyoyin tazarar haihuwa domin gujewa zubar da ciki da gishiri.

(*). Samun Sauƙin Kaya: Samar da kayan tazarar haihuwa daga gwamnati domin samun sauƙi zai taimaka wajen rage yawan mace-macen da suka shafi zubar da ciki ba bisa ka’ida ba.

Ku Sani Cewa

Zubar da ciki da gishiri ko amfani da hanyoyin gida kamar lalle don zubar da ciki yana da haɗari sosai ga rayuwar mace. Ya kamata ki nemi taimakon likita don magance kowace matsala da ta shafi ciki. Hakanan, yin amfani da dabarun tazarar haihuwa zasu taimaka wajen hana samun ciki da ba a shirya ba cikin lafiya da kwanciyar hankali.

Ku tuna cewa, rayuwa tanada muhimmanci. Kada ku bar rashin sani ya jefaku cikin haɗari. Duk lokacin da kuka shiga damuwa, zai fi kyau ku nemi taimako daga masana lafiya shine mafita sahihiya.

Comments

Popular posts from this blog

Azabar Daren Farko

Azabar Daren Farko: Da Dalilin Dake Kawo Haka. Daren farko na aure ya kasance wani dare ne mai matukar muhimmanci ga amarya da ango, duk da cewa cike yake da fargaba, jin kunyar juna, dama kuma jindaɗi ga sababbin ma'aurata. Daren ranar farko na cike da farinciki da annashuwa na shiga sabon babin rayuwa. Sai dai kash! wasu amaren suna tsoron azabar daren farko , baku da laifi kunsan ance dama Allah ɗaya gari banbam domin kuwa wasu ma'auratan kan sha dadi a wannan lokaci wasu kuwa kan fuskanci ƙalubale da wahala a wannan lokaci.  Kafin dai in wuce ina yi muku lale maraba da shigowa wannan shafin ilimi nawa kuma zanyi bayani dalla-dalla dangane da azabar daren farko, dalilan dake kawo azabar daren farko, yadda amarya zata shawo kan matsalar, da kuma hanyoyin da ya kamata amarya da ango subi domin tabbatar da cewa daren farkonsu ya kasance mai cike da daɗi da kuma kwanciyar hankali. Menene dalilin da yasa Daren Farko yakan zama mai wahala ne? Abubuwa da dama sukan iya kawo azabar ...

Wasa Da Nonon Amarya A Daren Farko

Wasa da Nonon Amarya a Daren Farko: Ranar daren farko rana ce ta musamman ga rayuwar auren sabbin ma’aurata, domin tana matukar tasiri wajen gina soyayya da amincewa tsakanin amarya da ango tun daga tushe. Daga cikin abubuwan dake ƙara ƙayatar da daren wannan rana shine sanin sirrin wasa da nonon amarya a daren farko— wanda hakan ke kawo jindaɗi da nishadi ga ma’aurata idan aka yishi da hikima. A cikin wannan post nawa ni malamar mata ta wannan gida, zan tattauna sannan nayi bayani akan yadda ake wasa da nonon amarya a daren farko, muhimmancinsa, hanyoyin da za'a bi don jin daɗin mu'amala da juna, da abubuwan da ya kamata a kiyaye. Meyasa Wasa da Nonon Amarya A Daren Farko Yake Da Muhimmanci? Wasa da nonon mace yana da muhimmanci saboda: (*). Kawo Nishaɗi da Jindaɗi – Nonon mace yana da yawan jijiyoyi masu sanya mace jin daɗi yayin shafa su, musamman idan ka iya shafawa da tsotsewa cikin salo da iyawa. (*). Ƙarfafa Soyayya – Wasa da nonon amarya a daren farko yana taimakawa waj...

Kuka A Daren Farko

Menene dalilin da yasa mata keyin kuka a daren farko? Daren farko na aure musamman ga amare wani lokaci ne mai cike da tunanin yan’uwa da kuma fargaba, wanda hakan na iya kawo kuka a daren farko. Sannan kuma akwai   jin daɗi, da kuma sauye-sauyen rayuwa, wanda yarinya bata zama gani ba. Ga wasu amaren, wannan rana ta farko takan iya haifar da kuka – wanda kan faru saboda dalilai daban-daban da suka shafi nutsuwar zuciya, yanayin sabo na amaraya, ko ma wasu abubuwa masu kama da haka. A cikin wannan rubutu mai taken kuka a daren a daren farko nawa ni malamar mata ta wannan gida mai aminci, zanyi bayani mai kyau akan dalilan da ke haifar da kuka a daren farko, da kuma yadda maza angwaye za su fahimci lamarin, da kuma hanyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da cewa daren farko ya kasance mai kyau ga duka ma’auratan, wato amarya da ango. Ga wasu dalilan da ke sa amare kuka a daren farko Bugun zuciya (sakamakon rashin sabo) Amare da yawa na iya yin kuka a daren farko, saboda ras...