Yadda Ake Shagwaɓa a Soyayya Domin Yan'mata: Soyayya itace masu iya magana suke cewa ruwan zuma. Wato tafi daɗi idan kasha sannan kaba masoyi. Shagwaba a soyayya wani bigire ce da ke kawo nishadi da jindadi a zuciyar masoya, musamman idan kin iya gudanar da ita cikin salo na kulawa da fahimtar sahibinki. Yawanci gaskiya mata aka fi sani da shagwaba a soyayya domin dama ko ban faɗa ba, tofa shagwaba a soyayya tafi dacewa daku mata. Wasu lokutan maza suna yin shagwaba a soyayya kuma shagwaban maza sai ta baki dariya domin wasu kwata-kwata basu iya ba, amma wasu mazan suna iya shagwaba a soyayya yadda ya kamata. To dama dai ance kowa da kiwon daya karbe shi. Ɗaya daga cikin hanyoyin da ake kara danƙon ƙauna tsakanin masoya shine shagwaɓa a soyayya. Ita kuwa Shagwaɓa a soyayya ba wani abu bace illa wata dabara da ake yi ta salon magana ko motsin jiki domin neman kulawa ta gaggawa daga masoyiya, wato malam shagwaba a soyayya yan'mata suna yinta ne domin ka kula dasu cikin gaggawa wa...
Aminiya blog is your go-to platform for insightful and engaging content. From expert health tips and relationship advice to thought-provoking book reviews and the latest news updates, we cover it all.